Lahadi 19 Yuli 2026 - 00:49
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (60) | Illolin Kungiyoyin Karkata da Yadda Ake Tunkarar Su

Hauza/ Duk da yawan ƙiyayyar da ake yi wa koyarwar addini, kulawa da imani da Mahdawiyya na ci gaba da ƙaruwa a kowace rana. Wannan ƙaruwa ta sha'awa da jin buƙatuwa a fannonin hankali da zuciya, duk da cewa al'amari ne mai matuƙar albarka, sai dai a lokaci guda ya sa, duk da sahihai kuma zurfafan koyarwa, wasu ƙungiyoyin karkata ma sun bayyana, suka kuma jawo hankalin wasu mutane marasa zurfin fahimta ko masu mugun nufi na wani ɗan lokaci.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, ana gabatar muku da jerin darussan Mahdawiyya masu taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yaɗa koyarwa da ma'arifar da suka shafi Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), ga ku masu daraja.

Illolin Ƙungiyoyin Karkata A Tattaunawar Mahdawiyya

Duk da yawan ƙiyayyar da ake yi wa koyarwar addini, kulawa da imani da Mahdawiyya na ci gaba da ƙaruwa a kowace rana. Wannan ƙaruwa ta sha'awa da jin buƙatuwa a fannonin hankali da zuciya, duk da cewa al'amari ne mai matuƙar albarka, sai dai a lokaci guda ya sa, tare da sahihai kuma zurfafan koyarwa, wasu ƙungiyoyin karkata ma suka bayyana, suka kuma jawo hankalin wasu mutane marasa zurfin fahimta ko masu mugun nufi na wani ɗan lokaci.

Waɗannan ƙungiyoyin karkata, abin takaici, suna haifar da wasu munanan sakamako kamar haka:

Rashin Tabbaci A Cikin Imanin Addini

Da alama mafi girman illar waɗannan karkacewar ita ce haifar da girgiza da raunin imanin addini da mazhaba a cikin mutane. Wannan kuwa babban zunubi ne da ba za a gafarta ba, wanda yake cikakken misalin faɗin Allah Madaukakin Sarki:

"Suna kautar da mutane daga hanyar Allah...". (Suratul Hud, aya ta 19).

Lalata Jarin Basira Da Tunani

Babu shakka, a yau mazhabar Ahlul Baiti (A.S.) tana buƙatar masana da masu tunani fiye da kowane lokaci a fannoni daban-daban. Rasa irin waɗannan mutane saboda faɗawarsu cikin ƙungiyoyin karkata da kuma asarar ƙarfin tunaninsu, babbar hasara ce.

Me Ya Kamata A Yi Don Fuskantar Ƙungiyoyin Karkata?

1. Hanyar Ilimi

Amfani Da Sahihan Ilimi

Ilimi shi ne farkon kowane aiki. Rashin sanin sahihiyar koyarwar Mahdawiyya shi ne babban dalilin samuwar waɗannan ƙungiyoyin karkata. Saboda haka mataki na farko na kuɓuta daga irin waɗannan ƙungiyoyi shi ne ƙara samun sahihan bayanai.

Mafi muhimmancin hanyar samun wannan ilimi ita ce riƙo da ayoyin Alƙur'ani da ingantattun ruwayoyin Ma'asumai (A.S.). Don haka, a ɓangaren ilimi da fahimta, masu kishin wannan fage dole ne su shiga cikin hikima, tsari da ƙwarewa, su kuma sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata.

Isar da wannan ilimi yana da ginshiƙai guda biyu:

Na farko: sanin sahihai kuma asalan ma'arifar Mahdawiyya.

Na biyu: sanin karkace-karkacen, siffofinsu da kuma illolinsu.

Tsara Tsarin Mahdawiyya na Bai-Ɗaya

Babu shakka rashin daidaito tsakanin sassa daban-daban na al'adun addini yana samar da damar yaɗuwar karkacewa. Duban batutuwan Mahdawiyya ta fuskar da ta takaita ko ta ɓangare-ɓangare na daga cikin manyan dalilan samuwar waɗannan ƙungiyoyin karkatattu.

Amma duban ma'arifar Mahdawiyya ta hanya mai faɗi da tsari na gaba ɗaya daga masu kula da al'amuran al'adu, walau malamai ko masu ilimi, cikin haɗin kai, zai iya zama katanga mai ƙarfi da ba za a iya ketare ta ba wajen hana samuwar irin waɗannan ƙungiyoyi da ci gaba da ayyukansu.

2. Hanyoyin Aiki

Bayyana Gaskiya Da Haifar Da Hankali

Babu shakka girman illolin waɗannan ƙungiyoyin karkata ba zai bar damar yin sakaci ko sassauci da su ba. Domin waɗannan karkata sun fi miyagun ƙwayoyi muni; domin miyagun ƙwayoyi suna lalata jikin mutum ne, amma waɗannan karkata suna lalata ruhin mutane ne. Kuma babu wanda zai yarda a yi sassauci ga masu jefa matasa cikin miyagun ƙwayoyi.

Saboda haka wajibi ne ga kowa, musamman masu ilimi a cikin al'umma, su yi amfani da duk wata dama wajen tona asirin waɗannan ƙungiyoyi tare da faɗakar da matasa domin su nisanci tarkonsu.

Rushe Tushen Karkata 

A inda nasiha da kyakkyawar shawara ba su haifar da sakamako ba, mafi dacewar mafita ita ce tsayawa kai tsaye wajen fuskantar waɗannan ƙungiyoyin karkata da kuma rushe tushen karkacewarsu.

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ciro daga littafin "Darsnameh Mahdawiyyat", wanda Khodamurad Salimiyan ya rubuta, tare da ɗan gyara kaɗan

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha